ASIRIN WASU GWAMNONIN NIGERIA YA TONU
ASIRIN WASU GWAMNONIN NIGERIA YA TONU Zanga-zangar ENDSARS ta bar baya da kura, yanzu sun koma farfasa dakin ajiyar abinci a wasu jihohin Nigeria suna kwasar abinci na tallafin Coronavirus wanda shugaba Muhammadu Buhari ya bawa gwamnanoni domin su rabawa talakawa amma wasu gwamnonin suka ki rabawa Ina tuna lokacin da Ministar jin kai Hajiya Sadiya Umar Farouk ta bada sanarwan cewa gwamnatin shugaba Buhari ta kashe biliyoyin Naira wajen sayan abincin tallafi na Coronavirus, amma a lokacin aka dinga tsine mata ana karyatata cewa ba'a ga abincin ba, ita ma yau Allah Ya wanke ta Ga abinci nan shugaba Buhari ya bayar a baku, amma wasu miyagun gwamnoni sun boye sun barku da jin haushin shugaba Buhari kuna ta zaginsa ya kawo yunwa, gashi nan asirin mugayen gwamnonin ya fara tonuwa Wannan zanga-zangar ENDSARS ta yaye wa masu hankali duhun sharri da aka yiwa shugaba Buhari, yanzu masu hankali sun fahimci gaskiya, hakika shugaba Buhari alheri ne wa Nigeria Fasa gidan ajiyar abinci na gwamna