ASIRIN WASU GWAMNONIN NIGERIA YA TONU

ASIRIN WASU GWAMNONIN NIGERIA YA TONU

Zanga-zangar ENDSARS ta bar baya da kura, yanzu sun koma farfasa dakin ajiyar abinci a wasu jihohin Nigeria suna kwasar abinci na tallafin Coronavirus wanda shugaba Muhammadu Buhari ya bawa gwamnanoni domin su rabawa talakawa amma wasu gwamnonin suka ki rabawa


Ina tuna lokacin da Ministar jin kai Hajiya Sadiya Umar Farouk ta bada sanarwan cewa gwamnatin shugaba Buhari ta kashe biliyoyin Naira wajen sayan abincin tallafi na Coronavirus, amma a lokacin aka dinga tsine mata ana karyatata cewa ba'a ga abincin ba, ita ma yau Allah Ya wanke ta


Ga abinci nan shugaba Buhari ya bayar a baku, amma wasu miyagun gwamnoni sun boye sun barku da jin haushin shugaba Buhari kuna ta zaginsa ya kawo yunwa, gashi nan asirin mugayen gwamnonin ya fara tonuwa


Wannan zanga-zangar ENDSARS ta yaye wa masu hankali duhun sharri da aka yiwa shugaba Buhari, yanzu masu hankali sun fahimci gaskiya, hakika shugaba Buhari alheri ne wa Nigeria 


Fasa gidan ajiyar abinci na gwamnati laifi ne mai kama da cin amanar kasa a dokar Constitution, amma ni a fahimtata wannan ba laifi bane, dama hakkin talakawa ne wasu miyagun gwamnoni mugaye suka boye, wanda inda talakawa ba su daka wawa sun wawushe abincin ba wallahi a haka zai lalace daga karshe a kona


Allah Ka sakawa shugaba Buhari sakamako da gidan Aljannah

Allah Ka zaunar mana da Kasarmu Nigeria lafiya Amin <iframe data-aa="1508985" src="//ad.a-ads.com/1508985?size=728x90" scrolling="no" style="width:728px; height:90px; border:0px; padding:0; overflow:hidden" allowtransparency="true"></iframe>

Comments

Popular posts from this blog

Sassa Labaran DuniyaWasanniNishadiCikakkun RahotanniBidiyoShirye-shirye na MusammanShirye-shiryen rediyo Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Messi, Guardiola, Bailly, Bremer, Dzeko, Alaba

Musliman India