Sassa Labaran DuniyaWasanniNishadiCikakkun RahotanniBidiyoShirye-shirye na MusammanShirye-shiryen rediyo Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Messi, Guardiola, Bailly, Bremer, Dzeko, Alaba

 

Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Messi, Guardiola, Bailly, Bremer, Dzeko, Alaba

Lionel Messi

Har yanzu Manchester City na son daukar dan wasan Barcelona Lionel Messi idan kwangilarsa ta kare a bazara mai zuwa - kuma dan wasan na Argentina mai shekara 33 ka iya tafiya New York City FC. (Mundo Deportivo)

Sai dai Messi yana son samun tabbaci daga kocin City Pep Guardiola cewa dan wasan gaba Sergio Aguero zai ci gaba da zama a Etihad. (El Chiringuito via Mirror)

Guardiola, mai shekara 49, yana dab da sabunta zamansa na shekara biyar a kungiyar. (Telegraph)

Chelsea da Liverpool na duba yiwuwar zawarcin matashin dan wasan Barcelona Alejandro Balde, mai shekara 17, inda ake sa ran Ronald Koeman zai yi gaggawar saka shi a babbar tawagar kungiyar. (Sport via Express)

Daraktan wasanni na Ajax kuma tsohon dan wasan Arsenal Marc Overmars ya ce ya shirya domin fuskantar sabon kalubale tare da shugaban kungiyar Edwin van der Sar, a yayin da ake rade radin cewa mutanen biyu na shirin tafiya Manchester United(Mirror)

Liverpool da Everton na son daukar dan wasan Torino dan kasar Brazil Gleison Bremer, mai shekara 23. (Liverpool Echo)

Wakilin Eric Bailly ya gargadi Manchester Unitedcewa watakila dan wasan mai shekara 26 dan kasar Ivory Coast zai yi 'nazari' kan makomarsa idan halin da yake ciki bai sauya ba. (Calciomercato via the Sun)

Kocin Tottenham Jose Mourinho ya ce wa'adin zaman aron da dan wasan tsakiya mai shekara 21 Gedson Fernandes yake yi daga Benfica zai iya karewa a watan Janairu. (Sport TV via Sky Sports)

Magoya bayan Manchester City sun yi amannar cewa zai yi matukar kyau a dauko tsohon dan wasan kungiyar Edin Dzeko, mai shekara 34, don yin zaman matsakaicin lokaci idan aka bude kasuwar 'yan kwallo a watan Janairu. Yanzu dai dan wasan yana murza leda a Roma. (Manchester Evening News)

Juventus na kan gaba a fafutukar dauko dan wasan Bayern Munich dan kasar Austria David Alaba, mai shekara 28, wanda kwangilarsa za ta kare a bazara mai zuwa. (Tuttosport - in Italian)

Dan wasan Everton dan kasar Ivory Coast Jean-Philippe Gbamin, mai shekara 25, zai iya barin kungiyar a watan Janairu domin tafiya zaman aro bayan ya gaza taka rawar gani a Goodison Park. (Football Insider via Teamtalk)

Dan wasan Leeds da Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 24, ya ce abokin wasansa Patrick Bamford, mai shekara 27, yana dab da bin sa domin buga tamaula a matakin kasashen duniya. (Yorkshire Evening Post)

Shahararren dan wasan Liverpool Sir Kenny Dalglish ya yi amannar cewa kocin kungiyar Jurgen Klopp zai samu kyakkyawar mafita a tsaron bayan kungiyar bayan raunukan da Virgil van Dijk da Joe Gomez suka ji. (Liverpool Echo)

Mai yiwuwa Southampton ta sayar da Mohamed Elyounoussi ga Celtic a yayin da dan wasan mai shekara 26 dan kasar Norway yake wa'adinsa na biyu a kungiyar. (Hampshire Live)

Comments

Popular posts from this blog

ASIRIN WASU GWAMNONIN NIGERIA YA TONU

Musliman India