Real Madrid: Za ta buga wasa 11 daga nan zuwa karsen Disamba

  

<script type="text/javascript"> 
    var adfly_id = 25835799; 
    var adfly_advert = 'int'; 
    var frequency_cap = 5; 
    var frequency_delay = 5; 
    var init_delay = 3; 
    var popunder = true; 
</script> 
<script src="https://cdn.adf.ly/js/entry.js"></script> 


  Bayan da aka yi hutun mako biyu, Real Madrid za ta ci gaba da buga wasa ranar 21 ga watan Nuwamba, inda za ta fafata sau 11 daga nan zuwa karshen Disamba.

Real Madrid kawo yanzu ta yi wasa 11 tun fara kakar bana, inda ta buga karawa takwas a La Liga da uku a Champions League tun daga 20 ga watan Satumbar 2020.

Kawo yanzu Real ta ci wasan La Liga biyar da canjaras daya da rashin nasara biyu da ya hada da Cadiz da wanda Valencia ta doke ta 4-1 ranar 8 ga watan Nuwamba.

Hakan ne ya sa kungiyar ta Spaniya ke mataki na hudu da maki 16, kuma Real Sociedad ce ta daya da maki 20, sai Villareal ta biyu, sannan Athletico Madrid ta uku.

A gasar Champions League kuwa, Real tasha kashi a fafatawa daya da nasara daya da kuma canjaras daya, tana ta biyu a kan teburin rukuni na biyu da maki hudu.

Kungiyar Jamus, wato Borussia Munchengladbach ita ce kan gaba a runi na biyun.                                                            Daga nan zuwa karshen Disamba Real za ta kara a wasa 11, ciki har da takwas a La Liga da kuma uku a Champions League.

Kungiyar ta Spaniya za ta yi karawa uku kafin karshen watan Nuwamba da ya hada da wasa biyu a La Liga da daya a Champions League.

Wasanni 11 da Real Madrid za ta buga zuwa karshen Disamba:

Asabar 21 ga watan Nuwamba La Liga 

  • Villarreal da Real Madrid

Laraba 25 ga watan Nuwamba Champions League 

  • Inter da Real Madrid

Asabar 28 ga watan Nuwamba La Liga

  • Real Madrid da Alaves

Talata 1 ga watan Disamba Champions League 

  • Shakhtar da Real Madrid

Asabar 05 ga watan Disamba La Liga 

  • Sevilla da Real Madrid

Laraba 9 ga watan Disamba Champions League 

  • Real Madrid da Borussia M'gladbach

Lahadi 13 ga watan Disamba La Liga

  • Real Madrid da Atl Madrid

Laraba 16 ga watan Disamba La Liga

  • Real Madrid da Athletic Bilbao

Lahadi 21 ga watan Disama La Liga

  • Eibar da Real Madrid

Laraba 23 ga watan Disamba La Liga

  • Real Madrid da Granada

Laraba 30 ga watan Disamba La Liga

  • Elche da Real Madrid              
  • <script type="text/javascript"> 
        var adfly_id = 25835799; 
        var adfly_advert = 'int'; 
        var frequency_cap = 5; 
        var frequency_delay = 5; 
        var init_delay = 3; 
        var popunder = true; 
    </script> 
    <script src="https://cdn.adf.ly/js/entry.js"></script> 


                         

Comments

Popular posts from this blog

Sassa Labaran DuniyaWasanniNishadiCikakkun RahotanniBidiyoShirye-shirye na MusammanShirye-shiryen rediyo Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Messi, Guardiola, Bailly, Bremer, Dzeko, Alaba

ASIRIN WASU GWAMNONIN NIGERIA YA TONU

Musliman India